IQNA

Wani Bafaranshe Ya Wulakanta Alkur'ani Mai Tsarki

13:55 - October 07, 2010
Lambar Labari: 2007308
Bangaren kasa da kasa; A ci gaba da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da ake yi da sunan 'yancin bayyana ra'ayi a cikin kasashen turai, wani bafaranshe ya keta kur'ani mai tsarki, kuma yasa hotunan a cikin shafin internet.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa an bayyana cewa, a ci gaba da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da ake yi da sunan 'yancin bayyana ra'ayi a cikin kasashen turai, wani bafaranshe ya keta kur'ani mai tsarki, kuma yasa hotunan a cikin shafin yanar gizo.

Bayanin ya ci gaba da cewa hakan ya z one a daidai lokacin da kyamar addinin muslunci da muslmi ke ci gaba da karwa a cikin kasashen yammacin turai, sakamakon damar da hukumominsu ska bayar na yin hakan ga duk mai so.

Bafaranshen ya kwashe kimanin sa'a daya yana keta takardun kur'ani mai tsarki kuma yana dauka da na'urar daukar hotuna, daga bisani kuma saka a internet.

Jin ra'ayin jama'a dai ya tabbatar da cewa al'ummar turai ba su san komai dangane da addinin muslunci ba, a kan haka suke gaba da shi bisa bakin jahilci.

668615




captcha