Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga kamfanin dillancin labaran Afp na kasar Fransa cewa, babban sakataren kwamitin cibiyar musulmin kasar Jamus (ZMD) ya nuna gamsuwa da furucin da ya fito daga bakin shugaban kasar Cristine Wolf dagane da wajabcin kare hakkokin musulmi a nahiyar turai.
Babban sakataren cibiyar musulmin Jamus Iman Mazik ya bayyana gamsuwarsa kan wannan furuci ne a cikin wata zantawa da ta hada shi da wata jaridar kasar mai suna Bild da ke fitowa kullum rana.
Ya bayyana cewa bayanin da Cristne Wolf ya yi a matsayinsa na shugaban Jamus da ke cewa wajibi ne a kiyaye hakkokin musulmi, wannan babban abin yabo ne.
Bayan yin wannan furuci an shugaban Jamus din musulmi da dama a kasar sun fito karara suna farin cikinsu da gamsuwarsu da wannan matsayi nasa.
668629