IQNA

Bincike Kan Koyarwar Kur'ani A Wasu Majami'oin Amurka

13:54 - October 07, 2010
Lambar Labari: 2007310
Bangaren kasa da kasa; Majami'ar First United Methodist da ke kasar Amurka ta bude ajujuwan samun masaniya kan kur'ani mai tsarki, da nufin mayar da martani ga masu hankoron tozarta addinin Musulunci ta hanyar wulakanta kur'ani mai tsarki.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na radiosawa cewa, majami'ar First United Methodist da ke kasar Amurka ta bude ajujuwan samun masaniya kan kur'ani mai tsarki, da nufin mayar da martani ga masu hankoron tozarta addinin Musulunci ta hanyar wulakanta kur'ani mai tsarki da wasu jahilan kiristoci suke yi.

Wannan majami'a ta dauki wannan mataki ne bayan da ta soki lamirin kiristocin da suke wulakanta kur'ani, inda ta bayyana cewa mai makon wulakanta kur'ani da kamata ya yi su san abin da ke cikinsa.

Majami'ar tana gayyatar musulmi da suke da masaniya kan kur'ani su zo su bayyana abin da ke cikinsa na ilmi ga mabiya addinin kirista da ke karkashin wannan majami'a.

668649



captcha