IQNA

Malumman Addinin Musulunci Sun Jaddada Wajibcin Fadada Yafewa

13:52 - October 07, 2010
Lambar Labari: 2008129
Bangaren siyasa da zamantakewa; malummai musulmi a kasar Afganistan da kuma wasu daga wasu kasashe da ke makobtaka da kasar ta Afganistan da suka halarci taron baya bayan nan a garin Hirat sun jaddada fadada hadin kai da yafewa irin ta addini a duniyar musulmi.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran daga reshensa na Afganistan bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Bakhtar ya watsa rahoton cewa: malummai musulmi a kasar Afganistan da kuma wasu daga wasu kasashe da ke makobtaka da kasar ta Afganistan da suka halarci taron baya bayan nan a garin Hirat sun jaddada fadada hadin kai da yafewa irin ta addini a duniyar musulmi.Gulam Faruk Huseini kakkakin kungiyar adddini a Hauza da ke yammacin Afganistan fdangane da wannan lamari ya bayyana cewa; wannan taro day a kwashe kwanaki hudu ana gudanar da shi tun ranar goma ga watan Mihr an samu halartar mutane dubu saba'in da biyar da suka hada da malumman addini a yankun daban daban na Afganistan da wasu kasashe masu makobtaka da Afganistan.


669711
captcha