IQNA

Bangarorin Kur'ani Da Na Addini Na Halartar Baje Kolin Kayan Sadarwa

12:46 - October 09, 2010
Lambar Labari: 2009014
Bangaren kasa da kasa, Masu gudanar da ayyuka a bangaren addini musamamn ma na kur'ani mai tsarki suna halartar taron baje kolin kayayyakin sadarwa na kur'ani mai tsarki da ake gudarwa a birnin Tehran.


A wata zantawa da ta hada shugaban baje kolin kayyakin sadarwar kur'ani a birnin Tehran, ya bayyana a wata zantawa da ta hada shi iqna cewa, masu gudanar da ayyuka a bangaren addini musamamn ma na kur'ani mai tsarki suna halartar taron baje kolin kayayyakin sadarwa na kur'ani mai tsarki da ake gudarwa.

Bayanin ya ci gaba da cewa dukkanin masu halartar wannan baje koli da ke gudana a matsayi na kasa da kasa, sun nuna gamsuwarsu da namijin kokarin da aka yi wajen wadata kasashen muslmi da kayan sadarwa masu inganci.

Daga cikin muhimman abubuwa da ake nunawa a wannan baje koli dai har da na'urori masu kwakwalwa, da aka saka musu shirye-shirye daban-daban na addini musamman ma na kur'ani.

670587




captcha