Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto shafin sadarwa na kamfanin dillancin labarn AFP na kasar Faransa an bayyana cewa, Wasu daga cikin jagororin addinai da aka safkar daga sama da suka hada da musulmi da kuma mabiya addinin kirista sun yi kakkausar suka kan kyamar musulmi da ake nunawa.
Bayanin ya ci gaba da cewa jagororin addinan sun sanar da hakan ne a cikin wani bayani na hadin gwiwa da suka fitar, inda suka tabbatar da cewa kyamar musulmi ko tsangwmarsu ba ya cikin wani addini.
Tun bayan da wani mai kiran kansa malamin kirista a kasar Amurka ya sanar da ranar 11 ga watan satumba a mtsayin ranar kone kur'ani, kyamar musulmi ke ta karuwa a kasashen turai.
670554