IQNA

Musulmi Da Kiristoci Sun Yi Gargadi Kan Yahudantar Da Qods

22:50 - October 09, 2010
Lambar Labari: 2009471
Bangaren kasa da kasa, Wasu daga cikin fitattun musulmi da kiristoci sun yi gargadi kan duk wani yunkurin yahudantar da Qods da yahudawan sahyuniya ke ta hankoron yi.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga jaridar Alkhalij ta haddiyar daular larabawa an bayyana cewa, wasu daga cikin fitattun musulmi da kiristoci sun yi gargadi kan duk wani yunkurin yahudantar da Qods da yahudawan sahyuniya ke ta hankoron yi a cikin 'yan lokutan nan.

Bayanin ya ci gaba da cewa dukkanin bangarorin musulmin da kiristocin sun sanar da hakan ne a cikin wani bayani na hadin gwiwa a gaban wani taron manema labarai a birnin na Qods mai alfarma.

Inda suka bayyana cewa masallacin Qods wuri mai alfarma na dukakkanin mabiya addinai da aka safkar daga sama, a kan haka babu wani dalili da zai sanya yahudawa sun mayar da shi mallakinsu.

670544




captcha