Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an gudanar da gasar hardar kur'ani mai tsarki a kasar Burkina Fasso wanda cibiyar kula da harkokin kur'ani mai tsarki ta kasar ta dauki nauyin shiryawa a birnin Wagadugu fadar mulkin kasar.
Wannan gasa dai tana daya daga cikin muhimmai irinta da ake gudanarwa a kasashen yammacin nahiyar Afirka, kuma na kasa gasar ne zuwa kashe uku daidai da dukkanin bangarorin da aka gudanar da gasar a cikinsu.
Daga wadanda suka yi alkalancin gasar akwai Hassan gajaga, wanda shi ne ya jagoranci tawagar alkalan, akwai kuma wasu daga cikin wadanda suka sanya ido kan yadda gasar ta gudana.
671216