IQNA

Taron Kasa Da Kasa Kan Sirar Ma'aiki (SAW) A Kasar Turkiya

13:40 - October 10, 2010
Lambar Labari: 2009941
Bangaren kasa da kasa, An fara gudanar da wani zaman taro domin bahasi kan sirar manzon Allah (SAW) a birnin Istanbul fadar mulkin kasar Turkiya a matsayi na kasa da kasa.



Kamfanin dillancin labaran kur'ani mai tsarki na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na samanyoluhaber cewa, an fara gudanar da wani zaman taro domin bahasi kan sirar manzon Allah (SAW) a birnin Istanbul fadar mulkin kasar Turkiya a matsayi na kasa da kasa.

Wannan zaman taro yana samun halartar masana daga sassadaban-daban na kasashen musulmi da na larabawa da sauran kasashen duniya, kamar yadda taron ke samun halartar manyan jami'ai na gwamnatin Turkiya.

Wasu daga cikin mahlartar sun gabatar da jawabai a zaman taron, da suka hada da Ali Bardako shugaban cibiyar kula da harkokin addinai ta kasar.

670955



captcha