Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na baje kolin kayyaykin dijital an bayyana cewa, Jami'ar Al-mostafa (SAW) na halartar baje kolin kasa da kasa na hanyoyin sadarwar ta hanayar digital da ake gudanarwa a birnin Tehran..
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan baje koli na daya daga cikin irinsa mafi muhimmanci da ake gudanarwa a jamhuriyar Musulunci ta Iran a kowace shekara, inda kamfanoni daban-daban sukan baje kayayyakin sadarwa.
Yanzu haka dai jami'ar Al-mostafa (SAW) ta halarci wurin kuma ta baje wasu daga cikin kayyakin da za a iya yin amfani da su domin sadarwar Musulunci a kasashe daban-daban.
671057