IQNA

Fatawar Jagoran Iran Na Da Muhimmanci Wajen Kusanto Da Mazhabobi

13:39 - October 10, 2010
Lambar Labari: 2009944
Bangaren kasa da kasa; Kakkin jami'ar Azhar ta kasar Masar ya bayayna cewa fatawar da jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamnei ya bayar kan haramcin tozarta matan manzo (ASW) da fitattun Ahlu sunna, tan ada muhimamnci.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na jazeera net an bayyana cewa kakkin jami'ar Azhar ta kasar Masar ya bayayna cewa fatawar da jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamnei ya bayar kan haramcin tozarta matan manzo (ASW) da fitattun Ahlu sunna, tana da muhimamnci wajen hada kan musulmi da kuma kusanto da mazhabobinsu.

Babban malamin jami'ar Azhar ya yi na'am da fatawar jagoran juyin juya halin muslunci Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, inda ya bayyana fatawar da cewa za ta taimaka wajen hada kan musulmi.

670999



captcha