Bangaren kasa da kasa, Za a gudanar da taron maulidin sayyid Fatimah Ma'asuma'a (SA) a birnin Vienna fadar mulkin kasar Austria, tare da halartar musulmin birnin.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin cibiyar Imam Ali (AS) cewa, za a gudanar da taron maulidin sayyid Fatimah Ma'asuma'a (SA) a birnin Vienna fadar mulkin kasar Austria, tare da halartar musulmin birnin na Vienna.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taron maulidi cibiyar muslunci ta birnin ce ta dauki nauyin shirya shi, da nufin raya ranaku masu albarka a cikin addinin muslunci, za a gudanar da jawabai dangane da rayuwarta mai albarka daga malamai daban-daban.
Sayyid Fatima Ma'asuma (SA) tana daya cikin 'ya yan limaman iyalan gidan manzon Allah (SAW) masu matsayi na musumman a cikin addinin muslunci, diya ce ga Imami, 'yar uwar Imami jikar Imami.
671071