Bangaren kasa da kasa, Kafofin yada labarai na muslunci suna halartar baje kolin kayayyakin sadarwar muslunci na kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin Tehran, tare da nuna wasu daga cikin irion wadannan kayayyki.
kamfanin dilalncin labaran iqna ya hbarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga bangaren gudanar da baje kolin kayan sadarwar muslunci cewa, Kafofin yada labarai na muslunci suna halartar baje kolin kayayyakin sadarwar muslunci na kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin Tehran, tare da nuna wasu daga cikin irion wadannan kayayyki na sadarwa.
Daga cikin kafofin sadarwa na musulmi da suke halartar wannan baje koli harda cibiyoyin hada mazhabobin muslunci ta hanyar sadarwa da ke gudanar da ayyukansu a kasar Rasha da kuma Afghanistan gami da Tajikistan.
Babbar manufar halartar cibiyoyin da ke kula da habbaka harkokin sadarwar Musulunci a kasashen daban-daban a wannan baje koli, ita ce kara tabbatar da hadin gwiwa da hadin kai tsakanin kafofin sadarwa.
671017