IQNA

Za A Sayar Da Kwafin Kur'ani Da Ya Yi Shekaru 300 A Jamus

14:40 - October 10, 2010
Lambar Labari: 2010022
Bangaren kasa da kasa; Za a sayar da wani kwafin kur'ani mai tsarki day a kwashe kimanin shekaru 300 a kasar Jamus, wanda yanzu haka an saka shi a kasuwa, kuma tuni masu bukatar sayensa suka fara tayi.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na Islamic Art Magazine an bayyana cewa, Za a sayar da wani kwafin kur'ani mai tsarki day a kwashe kimanin shekaru 300 a kasar Jamus, wanda yanzu haka an saka shi a kasuwa, kuma tuni masu bukatar sayensa suka fara tayawa.

Yanzu haka dai tayin farko da aka fara yi ya kai kudin yuro dubu 900 a matsayin tayin farko, wanda kuma ko shakka babu mutane da dama sun nuna sha'awarsu ta sayen wannan kur'ani, wanda ake sa ran kudinsa za su haura hakan.

A cikin shekara ta 2006 an sayar da wani kwamfin kur'ani makamnacin wannan da ya kai dala miliyan 10, kamar yadad aka sayar da wani a cikin 2007 dala miliyan hudu da dubu dari uku.

670963



captcha