Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Alyaum sabi ta kasar Masar an bayyana cewa gidan radiyon nan na kasar Masar da ke gudanar ad shirye-shirye da suka danganci kur'ani shi ne radiyon da ya fi kowane radiyo yawan masu saurare a kasar ta Masar.
Bayanin ya ci gaba da cewa shugaban gamayyar gidajen radiyoyi na kasar Masar shi ne ya sanar da hakan, inda ya ce an gudanar da jin ra'ayin jama'a ne a kasar ta Masar, wanda sakamakon hakan ne ya tabbatar da cewa wannan gidan radiyon ne kan gaba wajen masu saurare.
Sakamakon jin ra'ayin jama'ar ya tabbatar da cewa kimanin kashi 98 na kasar masar sun fi mayar da hankali wajen sauraren gidan radiyon kur'ani na kasar.
670799