IQNA

Aikin Kafofin Sadarwar Musulunci Shi Ne Yakin Kwakwalwa Da Makiya

8:25 - October 11, 2010
Lambar Labari: 2010322
Bnagaren kasa da kasa, A yau daya daga cikin muhimman ayyukan da suke gaban kafofin sadawar musulmi shi ne mayar da hankali wajen shiga kafar wando da makiya ta hanyar mayar da martani kansu da hikima.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na taron kasa da kasa kan ayyukan radiyo da taabijin na kasashen musulmi an habarta cewa, a yau daya daga cikin muhimman ayyukan da suke gaban kafofin sadawar musulmi shi ne mayar da hankali wajen shiga kafar wando da makiya ta hanyar mayar da martani kansu.

Taron wanda ake guadanarwa a babban dakin taruka na hukumar radiyo da talabijin din kasar Iran, wanda ke samun halartar masana daga sassa daban-daban na kasashen musulmi, yana yin tskaci ne kan muhimman ayyukan da musulmi ya kamata su mayar da hanakali kansu a wannan zamani ta fuskacin sadarwa.

Haka nan kuma a wajen taron an yi kira ga mayar da hanakali kan batun samar da hadin kai tsakanin al'ummar musulmi, tare da yin watsi da banbancin mazhaba ko abin da ya yi kama da haka.

672044



captcha