IQNA

Rayuwar Manzon Allah (SAW) Abin Koyi Ce Ga Rayuwar Dan Adam

17:02 - October 11, 2010
Lambar Labari: 2010939
Bangaren kasa da kasa, rayuwar manzon Allah (SAW) ita ce abin koyi ga dukkanin 'yan adam, kamar yadda bababn malami mai bayar da fatawa na kasar Ali Juma'a ya bayyana hakan.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran medya73 cewa, rayuwar manzon Allah (SAW) ita ce abin koyi ga dukkanin 'yan adam, kamar yadda bababn malami mai bayar da fatawa na kasar Ali Juma'a ya bayyana hakan a wani zaman taro da ake gudanarwa kan sirar ma'aiki a birnin Istanbul na kasar Turkiya.

Ya ce idan aka dubi sirar ma'aiki (SAW) tun daga kuruciyrsa har zuwa girmansa za a kyawawan dabi'u karamci gaskiya da rikon amanakamar yadda tarihi ya tabbatar, wanda kuma hatta makiyansa sun amince da hakan.

Taron na birnin Istanbul ana gudanar da shi ne a matsayi na kasa da kasa, da ke samun halartar masana da malamai daga kasashen musulmi da na larabawa.

671713




captcha