IQNA

Matar Gol Ta Kan Batun Takkadamar Da ake Yi Kan Hijabi

18:19 - October 11, 2010
Lambar Labari: 2010988
Bangaren siayasa da zamantakewa, Matar shugaban kasar Turkiya Abdullah Gol ta koka dangane da takaddamar da aka jawo kan batun hijabi a majalisar kungiyar tarayyar turai.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na akhbar alalam an bayyana cewa, matar shugaban kasar Turkiya Abdullah Gol ta koka dangane da takaddamar da aka jawo kan batun hijabi a majalisar kungiyar tarayyar turai da wasu bijiro da shi.

Bayanin ya ci gaba da cewa matar ta nuna matukar rashin jin dadinta dangane da yadda ake kokarin tauye hakkokin al'ummomi ba gaira ba sabar, domin kuwa a mahangarta batun hijabi lamari da ya shafi hakkin mutane wanda ya kamata kare musu shi.

Wasu daga cikin mambobi a kungiyar tarayyar turai sun jawo takaddama dangane da yadda mata suke saka hijabi a kasar Turkiya, duk da cewa babu wadda aka tilasta wa ta yi hakan.

672071




captcha