IQNA

Mai Bayar Da Fatawa Na Syria Ya Bijiro Da Batun Duniyar Musulmi

Bangaren al'adu da fasaha, A ci gaba da zaman tattaunawa a matsayi na kasa da kasa kan kan binciken ilmomin Musulunci da ake gudanarwa a Malazia, ana bijiro da muhimman batutuwa da suka danganci duniyar musulmi.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga jaridar tashrin an bayyana cewa, a ci gaba da zaman tattaunawa a matsayi na kasa da kasa kan kan binciken ilmomin Musulunci da ake gudanarwa a Malazia, ana bijiro da muhimman batutuwa da suka danganci duniyar musulmi baki daya.

Bayanin ya ci gaba da cewa babban malamin addini mai bayar da fatawa a kasar Syria ya bayyana cewa, dole a mayar da hankali kan abubuwa na asasi da suka shafi musulmi da kuma daukar matakan warware matsalolin da suka addabe su.

Taron dai yana samun halarta malamai da masana daga sassa daban-daban na duniyar mulsulmi da kuma kasashen larabawa, daga cikin abubuwan da aka bijiro da su hard a batun palastinu.

672119