Bangaren siayasa, Alkalin alkalan kasar Iran ya bayyana cewa kasashen yammacin turai su ne kan gaba waje danne hakkokin bil adama aduniya, duk kuwa da babatun da suke yi kan kare hakkokin dan adam.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga bangaren hulda da jama na ma'aikatar shari'a an bayyana cewa, Alkalin alkalan kasar Iran Ayatollah Larijaniya bayyana cewa kasashen yammacin turai su ne kan gaba waje danne hakkokin bil adama aduniya, duk kuwa da babatun da suke yi kan kare hakkokin mutane.
Bayanin ya ci gaba da cewa alkalin alkalan ya tabbatar da cewa akwai dalilai da dama da suke tabbatar da cewa babu inda aka take hakkokin dan adama kamar kasashen nahiyar turai, kuma abin da ya fi muni, akan take hakkin dan adam ne da suna kare hakkinsa.
Abin da ya faru da musulmi a cikin 'yan lokutan nan ya isa ya zama dalili, inda ake cin zarafinsu tare da tozarta addininsu, a lokaci guda kuma masu aikata hakan ana bayyana cewa suka da hakkin bayyana ra'ayinsu.
672182