IQNA

Makon Masallatai A Kasar Turkiya

Bangaren al'adu da fasaha : a kasar Turkiya an fara gudanar da makon masallatai a fadin kasar Turkiya kuma wannan mako ne na girmama masallatai da limaman juma'a a babban masallacin garin Sara Unu na kasar.

Kamfanin dillancin labarai Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran daga reshensa da ke Turkiya bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Alukah ta watsa rahoton cewa; a kasar Turkiya an fara gudanar da makon masallatai a fadin kasar Turkiya kuma wannan mako ne na girmama masallatai da limaman juma'a a babban masallacin garin Sara Unu na kasar. Muftin garin Sara Unu a wajen bukin kaddamar da makon Masallatai a fadin kasar ta Turkiya ya bayyana cewa; a wannan makon masallatai ya bukati masu yi wa addini hidima da su kara kokari da himma.

673760