IQNA

Taron Kasa Da Kasa Kan Tattali Arzikin Musulunci A Qatar

11:45 - October 13, 2010
Lambar Labari: 2012080
Bangaren kasa da kasa, Za a gudanar da wani taron harkokin tattalin arzikin kasashen musulmi a matsayi na kasa da kasa a birnin Doha na kasar Qatar, wanda shi ne irinsa na farko.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na Gulf Times cewa, Za a gudanar da wani taron harkokin tattalin arzikin kasashen musulmi a matsayi na kasa da kasa a birnin Doha na kasar Qatar, wanda shi ne irinsa na farko da za a gabatar.

Fira miniustan kasar ta Qatar Hamad bin Jasim bin Jabr shi ne zai jagoranci zaman taron, wanda babbar cibiyar harkkin kudi da kasuwanci ta kasar ta dauki shiryawa da gudanarwa.

Kasar Qatar dai tana daya cikin kasashen musulmi masu yawan iskar gas da kuma danyen man fetur a shimfide karkashin kasa, da take taka rawa a bangarori da dama na tattalin arzikin duniya.

673611


captcha