Bangaren kasa da kasa, Majalisar malaman kasar ta shigar da kara kan rundunar 'yan sanda birnin Moscow, sakamakon hana musumi isa babban masallacin juma'ar birnin dmin gudanar da sallar juma'a ta wannan mako.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sarawa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran Interfax cewa, majalisar malaman kasar ta shigar da kara kan rundunar 'yan sanda birnin Moscow, sakamakon hana musumi isa babban masallacin juma'ar birnin dmin gudanar da sallar juma'a.
A cikin wani bayani da majalisaar malaman ta fitar an bayyana cewa 'yan sandan birnin Moscow sun tare wasu daga cikin muhimman hanyoyin da suke babban masallcin juma'a na birnin Moscow, lamarin da ya tilasta da dama yin salla a nesa da masallacin.
Majalisar malaman ta shigar da kara da nufin a gudanar bincike kan dalilan da suka 'yan sandan daukar wannan mataki na takura wa musulmi tare da hana su gudanar da ibadarsu cikin 'yanci.
673558