Bangaren kasa da kasa, Ma'anar Demokradiya a mahangar addinin Musulunci ta samo asali ne daga koyarwar alkur'ani mai tsarki, wato tabbatar da adalci da kare hakkokin al'umma a cikin mulki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na kamfanin dillancin labaran kuna na kasar Kuwait an bayyana cewa, malamin jami'ar na bapalastine da ke zaune a kasar Jordan Nawar Alhusaini ya bayyana cewa, ma'anar Demokradiya a mahangar addinin Musulunci ta samo asali ne daga koyarwar alkur'ani mai tsarki, wato tabbatar da adalci da kare hakkokin al'umma.
Ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da wani jawabi da aka shirya dangane da matsayin demokradiyya a mahangar kasashen turai, da kuma yadda Musulunci yake kallon abin da ake kira demokradiyya.
Malamin ya jaddada cewa da dama daga cikin kasashen duniya suna raya cewa suna suna demokradiyya ne a cikin harkokin mulkin muslkinsu, amma a zahiri abin da suke yi ya yi hannun riga da abin suke rayawa.
675400