Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar yaum sabi ta kasar Masar an bayyana cewa, babban malamin mabiya addinin kirista na kasar Masar ya haramta wa yin amfanin da takardar izinin shiga ta Haramtacciyar Kasar Isra'ila domin ziyarar birnin Qods.
Bayanin ya ci gaba da cewa bababn malamin mabiya addinin kiristan na kasar ya bayayna cewa karbar visa daga gwamnatin yahudawa tamkar amincewa ne da halascinta, wanda kuma gwamnatin Isra'ila haramtacciya ce a mahangar addinin kirista.
Da dama daga cikin musumin kasar Masar sun fito karar sun bayyana gamsuwarsu da wannan mataki, inda suke ganin cewa ya yi daidai da abin da suka yi imani da shi na rashin halascin gwamnatin yahudawan.
675396