Bangaren kasa da kasa, Za a gudanar da wani zaman taro da aka bai wa take kur'ani da addinin muslunci da kuma koyarwar hukunce-hukuncen kur'ani da na addinin muslunci a kasar Amurka, a jahar Ilinia.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na rosaonline cewa, Za a gudanar da wani zaman taro da aka bai wa take kur'ani da addinin muslunci da kuma koyarwar hukunce-hukuncen kur'ani da na addinin muslunci a kasar Amurka, a jahar Ilinia da ke kudancin kasar.
Wannan taro dai cibiyar bunkasa fahimtar da sauran amutane addinin muslunci a kasar Amurka ta dauki nauyin shirya shi, da nufin kara wayar da kan musulmi kan hakikanin addininsu da kuma koyarwarsa.
Masu halartar wannan zaman taron sun nuna gamsuwarsu da yadda ake bayyana musu hakianin koyarwar addinin muslunci, ta yadda za su iya bayyana addinin ga masu bukatar samun masaniya kansa.
675365