Kamfanin dillancin Labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar kamfanin dillancin labarai na AFP ya watsa rahoton cewa: Muhammad Samak sakataren komitin kasa kan tattaunawa tsakanin Musulunci da kiristancin Labanon a ranar ashirin da biyu ga watan Mihr na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara a wani jawabi day a gabatar ya bayyana cewa; girmama kiristoci mazauna yankin gabas ta tsakiya wani nauyi da wajibi ne a shari'ance a addinin Musulunci. Wannan jawabin nasa ya tabbatar da cewa kasancewar kiristoci na rayuwa kafada da kafada day an uwansu musulmi a yankin gabas ta tsakiya wajibi ne kamar yadda kiristoci a Palasdinu da sauran yankunan da aka mamaye suna sahun gaba day an uwansu musulmi wajen yakar gwamnatin mamaye ta Haramtacciyar kasar Isra'ila.
675257