Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadawa na jaridar Gulf News an bayyana cewa, an nuna wasu tasoshi da aka kawata su da rubutun kur'ami mai tsarki a babban taron baje koli na kyakkyawan rubutun ayoyin kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa a birnin Dubai na haddaiyar daular larabawa.
Wannan shi ne karon farko da ake gudanar da irin wannan baje koli a kasar wanda ke samun halartar fitattun marubuta da suka shahara wajen kawata rubutun ayoyin kur'ani mai tsarki a kan alluna da sauransu.
An nuna da dama daga cikin abubuwan da aka rubuta da suke dauke da zayyanar ayoyin kur'ani mai tsarki, da suka hada da karmato gami da tasoshi da kuma wasu aluna na itace.
675639