IQNA

An Gano Wani Dadadden Kur'ani A Cikin Wata Majami'a Amurka

11:33 - October 17, 2010
Lambar Labari: 2014156
Bangaren kasa da kasa, An gano wata nushar kur'ani mai tsarki a wata majami'ar birnin Madfor a kasar Amurka, da aka kaddara shekarunsa a cikin majami'ar da cewa ya kai shekaru 300 da suka gabata.



Kamfanin dillancin labaran kur'ani mai tsarki na iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani labari daga shafin sadarwa na yanar gizo na The Boston Channel cewa, an gano wata nushar kur'ani mai tsarki a wata majami'ar birnin Madfor a kasar Amurka, da aka kaddara shekarunsa a cikin majami'ar da cewa ya kai shekaru 300 da suka gabata ana ajye da shi.

Bayanin ya ce ana adana kur'anin ne a dakin karatu na David Scd da ke cikin majami'ar, inda ake ajiye dadaddin littafai da wasunsu sun haura daruruwan shekaru, daga ciki kuwa har da wannan kur'ani da aka bayyana.

Wani masanin tarihi ya bayyana cewa, tun bayan juyin juya halin da aka yi a kasar Amurka a cikin shekarar 1759, fada Scod ya samu wannan kur'ani, domin yin mudala'a kan addinin muslunci.

675807





captcha