IQNA

Shekhul Azzahar Ya Yi Watsi Da Kafirta Yan Shi'a

Bangaren kasa da kasa' Ahmad Altaib sheikhul Azzahar ya yi watsi da matakin da wasu tashoshin tauraron dan adam ke dauka na kafirta yan shi'a kuma cimma burin siyasa na haddasa sabani tsakanin yan shi'a da sunna shi ne babban burinsu.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokkin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta Masarawiya ya watsa rahoton cewa; Ahmad Altaib sheikhul Azzahar ya yi watsi da matakin da wasu tashoshin tauraron dan adam ke dauka na kafirta yan shi'a kuma cimma burin siyasa na haddasa sabani tsakanin yan shi'a da sunna shi ne babban burinsu.Ahmad Altaib a wata tattaunawa ce da ya yi da jaridar kasar labanon ta Nahar a ranar ashirin da uku ga watan Mihr na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya ya jaddada cewa; babu wani dalili da fahimta ta kur'ani da sunnar ma'aiki tsira da amincin Allah ya amince da shi da alayan gidansa na kafirta yan shi'a .

675570