Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman taro a matsayi na kasa da kasa a birnin Karbala mai afarma da aka baiwa take makon kur'ani, da zai samu halartar wakilai daga kasashe 20.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Nun an bayyana cewa, za a gudanar da wani zaman taro a matsayi na kasa da kasa a birnin Karbala mai afarma da aka baiwa take makon kur'ani, da zai samu halartar wakilai daga kasashe ashirin.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro za a gudanar da shi a cikin farfajiyar hub aren Imam Hussain (AS) da ke birnin na karbala mai alfarma, wanda cibiyar kua da ayyukan musulunci ta mabiya mazhabar shi'a a kasar Iraki ta dauki nauyin shiryawa.
Yanzu haka dai cibiyar ta bayyana cewa da zaran an kammala dukkanin shirye-shirye dangane da yadda za a gudanar da zaman za asanar a hukumance.
675734