Bangaren al'adu da fasaha, An gudanar da wani taron baje kolin kayayyakin al'adu da ilmi a kasar Zimbabwe, wanda cibiyar kula da bunkasa harkokin al'adu ta Iran ta dauki nauyn shiryawa a birnin Harare.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani mai tsarki na Iqna ya habarta cewa, an gudanar da wani taron baje kolin kayayyakin al'adu da ilmi a kasar Zimbabwe, wanda cibiyar kula da bunkasa harkokin al'adu ta Iran ta dauki nauyn shiryawa a birnin Harare fadar mulkin kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa a wani labari da ya nakalto daga bangaren yada abaransa na gabacin Afirka an bayyana cewa, wannan baje koli wanda shi ne irinsa na farko a kasar ta Zimbabwe, ya samu karbuwa daga al'ummar kasar.
Daga cikin abuuwan da aka nuna har wasu littafai da aka rubuta kan rayuwar matasa, da yadda musulunci ya baiwa matasa damar yin amfani da koyarwar musulunci.
676978