Bangaren aladu da fasaha, Shugaban bangaren bunkasa harkokin al'adu na karamin ofishin jakadancin Iran a Birtaniya ya bayyana cewa an fara gudanar da baje koli na littafan da firdausi ya rubuta.
Kamfanin dillancin abaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga wasu shafukan sadarwa an bayyana cewa, Shugaban bangaren bunkasa harkokin al'adu na karamin ofishin jakadancin Iran a Birtaniya ya bayyana cewa an fara gudanar da baje koli na littafan da firdausi ya rubuta na wakoki da ilimi.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan baje koli yana samun halartar masana daga sassa daban-daban na kasar da suke son gane wa idanunsu kan irin rubuce-rubucen da shahararren malamin ya yi.
Yanzu haka dai ana nuna akasarin littafan day a rubuta, da kuma nuna wasu daga cikin baitukan wakokinsa akan wasu alluna da aka kawata, kuma aka saka su a cikin wasu sandukai na gilashi.
676105