Bangaren kasa da kasa; an fara ayyukan gina garin maziyartan Imam Huseini (AS) da zummar yi wa maziyarta hidima da ke fitowa daga gurare masu nisa wajen garuruwar Najaf Da Karbala'a.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna mai kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar labarai ya watsa rahoton cewa; an fara ayyukan gina garin maziyartan Imam Huseini (AS) da zummar yi wa maziyarta hidima da ke fitowa daga gurare masu nisa wajen garuruwar Najaf Da Karbala'a.Wannan shiri na kaddamar da wannan gari na maziyarta da ke fitowa daga yankuna daban-daban na kasar Iraki da kuma wasu kasashe da ke makobtaka da Iraki musamman Iran da hakan zai taimaka matuka gaya wajen kyautata rayuwar maziyartan.
677561