IQNA

Taro Kan Mu'ijizar Ilimi Ta Kur'ani Da Sunnar Ma'aikin Allah (SWA) A Madina

Bangaren kasa da kasa; A birnin Madina ,birnin Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da iyalan gidansa an fara gudanar da taro kan irin mu'ijizojin Ilimi da ke dunkulai a cikin kur'ani mai girma da sunnar ma'aiki kuma an samu halartar gungun mata masu ayyukan da suka shafi Kur'ani kuma tunranar ashirin da biyar ga watan Mihr na wannan shekara aka bude taron.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna mai kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ta naklato daga jaridar Sabak ta hanyar na'ura ya watsa rahoton cewa; A birnin Madina ,birnin Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da iyalan gidansa an fara gudanar da taro kan irin mu'ijizojin Ilimi da ke dunkulai a cikin kur'ani mai girma da sunnar ma'aiki kuma an samu halartar gungun mata masu ayyukan da suka shafi Kur'ani kuma tunranar ashirin da biyar ga watan Mihr na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara ta hijira shamsiya aka bude taron. Kuma a wannan taro an samu halartar wasu masana day an jami'a a birnin Madinan.

677455