IQNA

An Bude Kofofin Masallatan Kaliforniya Ga Wadanda Ba Musulmi Ba

Bangaren kasa da kasa: komitin musulmi na Kaliforniya a bangaren kuduncin wannan lardi a ranar ashirin da biyar ga watan Mihr na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara na hijira shamsiya ta bude kofofin Masallatai ga wadanda ba musulmi ba.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna mai kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar watsa labarai ta Redlands Daily Facts ya watsa rahoton cewa; : komitin musulmi na Kaliforniya a bangaren kuduncin wannan lardi a ranar ashirin da biyar ga watan Mihr na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara na hijira shamsiya ta bude kofofin Masallatai ga wadanda ba musulmi ba.Bayan ga masallatan an kuma bude cibiyoyin Musulunci a yankin kuduncin lardin na Kaliforniya na Amerika kuma an samu dubban mutane wadanda ba musulmi da su ka ziyarci masallatan domin kara samun masaniya da addini da al'adu na Musulunci a masallatai da cibiyoyin addini.


677444