IQNA

Wajibi Ne Mutanen Duniya Su San Matsayin Musulunci Kan Harkar Kudi

10:45 - October 19, 2010
Lambar Labari: 2015644
Bangaren kasa da kasa, Shugaban bankin bunkasa hakokin tattaln arziki na kasashen musulmi Ahmad Muhammad Ali ya bayyana cewa, wajibi ne mutanen duniya su samu masani kan matsayin musulunci dangane da harkokin kudi.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Iqtisadiyyah ta kasar Saudiyya cewa, shugaban bankin bunkasa hakokin tattaln arziki na kasashen musulmi Ahmad Muhammad Ali ya bayyana cewa, wajibi ne mutanen duniya su samu masani kan matsayin musulunci dangane da harkokin kudi da tattalin arziki.

Ahmad Muhammad ya ce addinin muslunci yana da kyakkyawan tsari kan harkokin kudi da tatlin arziki wanda ya kamata mutanen duniya su samu masaniya kansa, wanda ko shakka babu hakan zai taimaka ma tattalin arzikin duniya.

Bankin bunkasa harkokin musulunci na duniya yana da shirye-shrye da yake fatan kaddamarwa da zasu taimaka harkokin tattalin arzki na duniya a nan gaba.

677605
captcha