IQNA

Za A Gudanar Da Gasar Karatun Kur'ani A Birnin Moscow

13:38 - October 20, 2010
Lambar Labari: 2016139
Bangaren kasa da kasa, Za a gudanar da wata gasar kur'ani ta kasa da kasa a birnin Moscow na kasar Rasha, wadda kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta shirya tare da hadin gwiwa da majalisar malamai musulmi na kasar Rasha.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga jaridar yaum sabi ta kasar Masar an bayyana cewa, za a gudanar da wata gasar kur'ani ta kasa da kasa a birnin Moscow na kasar Rasha, wadda kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta shirya tare da hadin gwiwa da majalisar malamai musulmi na kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasa za ta samu halartar makaranta da mahardata kur'ani mai tsarki daga kasashen duniya daban-daban, da suka hada da kasashen musulmi da na larabawa.

Babbar manufar gudanar da wannan gasa dai ita ce kara karfafa dankon zumuntaka tsakanin musulmi da kuma al'ummar kasar rasha, tare da karfafa cibiyoyi addini musussaman na kur'ani da ke kasar.

678133








captcha