Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Al-dastur cewa, babban sakataren gudanarwa na kungiyar PLO ya bayyana cewa Isra'ila tana shirga wa duniya karya kan batun tattaunawar sulhu da zaman lafiya tsakaninta da bangaren palastinawa da aka dakatar.
Bayanin ya ci gaba da cewa sakataren kungiyar ya bayyana cewa palastinawa sun koma ga tattaunawa ne da budaddiyar zuciya da nufin samun sulhu da zai kai ga kafa kasar palastinu mai cin gishin kanta.
Amma abin takaici shi ne yadda bangaren Isra'ila ke ta wasa da hankulan al'ummomin duniya kan wannan batu, inda Isra'ila ta tabbatar wa duniya cewa ita ce ba ta son tattaunawar sulhu tsakaninta da palastinawa.
680009