Bangaren kasa da kasa, Za agudanar da wani zaman taro kan hidima ga dan adam a birnin Istanbul fadar mulkin kasar Turkiya, tare da halartar wakilan kasashen duniya sama arba'in.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na medya 73 an bayyana cewa, za agudanar da wani zaman taro kan hidima ga dan adam a birnin Istanbul fadar mulkin kasar Turkiya, tare da halartar wakilan kasashen duniya sama arba'in da za su gabatar nasu jawaban.
Adadin mahalartar taron zai haura mutane dari uku, da suka hada da malaman addini da kuma masana daga kasashen musulmin daban-daban da na larabawa gami da kasashen Asia da ma na turai.
Wannan zaman taro dai zai mayar da hanakali kan muhimman batutuwa da suka shafi batun taimako ga bil adama, musamman ma a wannan lokaci da ake fuskantar ba'oi na dabi'a a kasashen duniya.
679997