Bangaren kasa da kasa, Shugaban haramtacciyar kasar Isra'ila Shemon Peres ya bayyana cewa ba tare da taimakon Amurka ba Isra'ila ba bu inda za ta, saboda haka Amurka da Isra'ila abu daya ne da ba su rabuwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na Muhit a yanar gizo an bayyana cewa, shugaban haramtacciyar kasar Isra'ila Shemon Peres ya bayyana cewa ba tare da taimakon Amurka ba Isra'ila ba bu inda za ta, saboda haka Amurka da Isra'ila abu daya ne da kowane ke karfafa daya.
Ya ci gaba da cewa da ba don irin taimakon da Amurka take baiwa Isra'ila ba, da hatta rayuwa ba za ta yiwu ba a cikin Isra'ila, saboda Amurka ita ce ke bai wa Isra'ila komai domin ci gaba da rayuwa.
Peres ya ce idan Isra'ila ta kawo karshe rikinta da palastinawa, za ta iya kafa wani babban kawance da Amurka domin su fuskanci Iran baki daya, domin kawo karshen tsarin Musulunci a Iran.
680005