IQNA

Wani Malamin Yahudawan Sahyuniya Ya Halasta Kisan Palastinawa

10:51 - October 23, 2010
Lambar Labari: 2017543
Bangaren kasa da kasa, wani malamin yahudawan sahyuniya ya bayar da fatawar halascin yin garkuwa da palastinawa a lokacin artabu, tare da saka su wuraren da ake aman wuta domin kashe su ba tare da wata matsala ba.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na Lobnan alan an bayyana cewa, wani malamin yahudawan sahyuniya ya bayar da fatawar halascin yin garkuwa da palastinawa a lokacin artabu, tare da saka su wuraren da ake aman wuta domin kashe su ba tare da wata matsala ba a mahangarsa.

Ya ci gaba da cewa babu wata matsala idan sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila sun yi amfani da palastinawa wajen yin garkuwar yaki, domin su kare kansu daga makiya.

Malamin yahudawan ya bayyana haka ne bayan bayar da wata fatawa makamanciyar hakan da ke halasta rayukan kanann yara palastinawa da wani malamin yahudawan ya bayar.

679993



captcha