IQNA

Za A Bada Horo Kan Musulunci Cikin Yaren Larabci A London

Bangaren kasa da kasa; daga ranar shidda zuwa goma ga watan aban da muke ciki na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya cibiyar kula da al'adu da Musulunci ta Birnin London za ta bada horo kan ilmomin da sanin addinin Musulunci a cikin harshen larabci musamman ga malamai wadanda ba larabawa ba.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Asesco ya watsa rahoton cewa; daga ranar shidda zuwa goma ga watan aban da muke ciki na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya cibiyar kula da al'adu da Musulunci ta Birnin London za ta bada horo kan ilmomin da sanin addinin Musulunci a cikin harshen larabci musamman ga malamai wadanda ba larabawa ba. Wannan taron bada horo ya samu tallafi ne daga hukumar ilimi da al'adu da bada horo ta Asesko da ke karkashin kungiyar hadin kan kasashen musulmi. Kuma wannan horo zai taimaka matuka gaya wajen binkasa ilimi da masaniya a tsakanin malaman masu koyar da larabci wadanda ba larabawa.


680377