IQNA

Bukin Yin Bankwana Da Gabatar Da Sabon Shugaban Hukumar Al'adu

Bangaren kasa da kasa; a yau biyu ga watan Aban na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya za a gudanar da bukin yin bankwana a dabra daya a gabatar da sabon shugaban hukumar da ke kula da yada al'adu da dangantaka ta Musulunci ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran karkashen jagorancin ministan al'adu.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa; a yau biyu ga watan Aban na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya za a gudanar da bukin yin bankwana a dabra daya a gabatar da sabon shugaban hukumar da ke kula da yada al'adu da dangantaka ta Musulunci ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran karkashen jagorancin ministan al'adu.Da misalin karfe goma na agogon kasar ne aka gudanar da wannan buki a Huseiniyar Alzahra (S) da ke cibiyar hukumar inda aka jinjinawa Mahdi Mustaphawi kan jan aikin day a gudanar a cikin shekarun da kuma gabatar da Muhammad baker Khurramshad a matsayin sabon shugaban hukumar.

680381