IQNA

An Nada Sabon Shugaban Cibiyar Bunkasa Al'adun Musulunci

17:40 - October 25, 2010
Lambar Labari: 2019581
Bangaren kasa da kasa, A yau ne aka nada sabon shugaban cibiyar bunkasa harkokin al'adun musulunci wanda ministan al'adu na kasar Iran ya nada a karo na hudu tun bayan kafa cibiyar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na cibiyar al'adu ta kasa an bayyana cewa, a yau ne aka nada sabon shugaban cibiyar bunkasa harkokin al'adun musulunci wanda ministan al'adu na kasar Iran ya nada a karo na hudu tun bayan kafa ta.

Sabon shugaban cibiyar da aka nada shi ne Muhammad Bakir Khoramshad, wanda daya ne daga jami'an cibiyar wanda ya dauki dogon lokaci yana gudanar da ayyuakansa kuma tare da samun yabo a matsayi na kasa.

An gudanar da gagarumin taro a yayin rantsar da shi a matsayin sabon shugaban cibiyar, taron da ya samu halartar manyan jami'an gwamnati da suka hada da ministan harkokin wajen kasar Iran Manochehr Mottaki.

681472





captcha