Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na santacruz an bayyana cewa za a gudanar da wani zaman taro na musulmin kasar Amurka a jahar California wanda zai samu halartar malamai da jagororin kungiyoyin musulmi na kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman zai kwashe tsawon makonni biyar ana gudanar da shi, inda za a gabatar da laccoci da kuma bayanai kan matsayin shari'a Musulunci, da yadda Musulunci yake kallon rayuwar dan adama ta fuskancin zamantakewa.
Babbar manufar gudanar da wannan zaman taro ita ce kara karfafa musulmi da basu masaniya kan addininsu, da kuma wayar da kan wadanda ba musulmi dangane da addinin Musulunci.
681230