Bangaren kasa da kasa, Za a gudanar da wani zaman taro da zai yi dubi kan harkokin tattalin arziki a mahangar addinin Musulunci a birnin bosi na kasar Faransa, wanda cibiyar nazari kan imomin addinin muslunci ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na IFESI an bayyana cewa, za a gudanar da wani zaman taro da zai yi dubi kan harkokin tattalin arziki a mahangar addinin Musulunci a birnin bosi na kasar Faransa, wanda cibiyar nazari kan imomin addinin muslunci ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a birnin.
Rahoton ya ce wannan zaman taro da za a gudanar zai mayar da hanakali wajen yin bahasi kan yadda addinin muslunci yake kallon batutuwa na harkar tattain arziki da kuma yadda ya kamata a tafiyar da su.
Taron dai zai samu halartar malaman jami'a gami da dalibai musamman ma masu nazari kan harkokin tattalin arziki a jami'oi daban-daban na kasar faransa, musamman ma daga birnin Paris.
A gobe za a fara gudanar da zaman taron kimanin karfe goma na safe, an dai bude wannan cibiya ne tun a cikin shekara ta 2001, da nufin bunkasa mahangar Musulunci.
681261