Bangaren kasa da kasa, An fara gudanar da shirin bayar da horo kan hardar kur'ani mai tsarki na dakarun gwamnatin kasar Yemen, gami da sauran jami'an tsaro da suke bukatar shiga cikin shirin da aka fara tun kwanaki biyu.
Kamfanin dillanci labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na kamfanin dillancin labaran kasar Yemen saba an bayyana cewa, an fara gudanar da shirin bayar da horo kan hardar kur'ani mai tsarki na dakarun gwamnatin kasar Yemen, gami da sauran jami'an tsaro da suke bukatar shiga cikin shirin da aka fara tun kwanaki biyu da suka gabata.
Babbar manufar gudanar shirin dai ita ce karfafa dakarun gwamnatin kasar wadanda dukkaninsu mabiya addinin Musulunci ne, ta yadda za su kara samun masaniya kan koyarwar kur'ani mai tsarki tare da hardace wasu daga cikin surorinsa, wannan dai shi ne karo na farko da ake gudanar da wannan shiri a kasar.
A lokacin gudanar da bukukuwan bude wannan shiri, ministan ma'aikatar da ke kula da ayyukan addini a kasar ya bayyana jin dadinsa dangane da yadda jami'an tsaro gami da sojoji suke mayar da hankali kan kur'ani mai tsarki.
681189