Bangaren kasa da kasa, An bude wata tashar radiyo da ke watsa shirye-shirye da harsuna daban-daban dangane da aikin haji a kasar Saudiyya, da nufin taimaka ma maniyyata da suke gudanar da ayyukan haji wajen sanin muhimman abubuwan da za su aiwatar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya naklato daga shafin sadarwa na kamfanin dillancin labaran nasij an bayyana cewa, an bude wata tashar radiyo da ke watsa shirye-shirye da harsuna daban-daban dangane da aikin haji a kasar Saudiyya, da nufin taimaka ma maniyyata da suke gudanar da ayyukan haji wajen sanin muhimman abubuwan da za su aiwatar a yayin aikin hajin.
Mataimakin baban daraktan talabijin da radiyo na kasar Saudiyya Ibrahim Safub ya bayyana cewa, wannan sabon radiyo zai watsa shirye-shiryensa ne a cikin harsunan larabci, turancin ingilishi, faransanci, yaren Indonesia farisanci da kuma Urdu gami da sawahili.
Gidan radiyon zai ci gaba da aiki ne har tsawon wata guda da za a gudnar da ayyukan hajji, kuma zai watsa shirye-shirye kimanin 96v a kowace rana ga alhazai domin yi musu hannuka mai sanda.
681095