Bangaren kasa da kasa, An gudanar da wani zaman taro a kasar faransa da zai yi dubi kan dangantakar musulmi da addinin muslunci, wanda kwamitin masallacin birnin Bondy ya dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na umma-united an bayyana cewa, za a gudanar da wani zaman taro a kasar faransa da zai yi dubi kan dangantakar musulmi da addinin muslunci, wanda kwamitin masallacin birnin Bondy ya dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a jiya.
Bayanin ya ci gaba da cewa wasu daga cikin mambobin kwamitin masalalcin sun jima suna gudanar da ayyukan fadadda fahimtar addinin Musulunci tsakanin mutanen kasar faransa wadanda ba mabiya addinin Musulunci ba.
Daga cikin abubuwan da zaman taron na jiya ya yi dubi a kansu har da wasu daga cikin maudu'an kur'ani mai tsarki da suke shiryar dad an a kan tafarkin rayuwa, domin komawa zuwa ga sa'ada ta hakika.
682227